Saturday, 30 March 2019

Banson takurawa mutane shiyasa nake sallar Juma'a a masallacin Villa>>Shugaba Buhari

A yayin da tawagar limaman addinin musulunci karkashin jagorancin farfesa Shehu Ahmad Galadanci suka kaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyarar taya murnar lashe zabenshi a jiya Juma'a, sun bukaci daya rika zuwa sallar Juma'a a babban masallacin Abuja, saidai shugaban yace wahalar da mutane ke shiga ciki ce baya so.Da yake bayar da amsa ga bukatar ta limaman, shugaba Buhari yace kunsan irin yanda tafiyar tawagar shugaban kasa take, idan zan fita sai an rufe wasu hanyoyi a hana mutane zirga-zirga wanda hakan yana takura rayuwarsu, to gujewa hakanne yasa na zabi yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa.

Limaman sun wa shugaban tuni akan hakkin talakawa akan shugaba kamar yanda yake a koyarwar manzon tsira(S. A. W). Sannan sun tayashi murnar cin zabe inda suka bayyana hakan a matsayin amincewar 'yan Najeriya domin kaisu mataki na gaba da kuma ci gaban ayyukan raya kasa da shugaban ya fara, kamar yanda sanarwar me magana da yawun shugaban, Femi Adesina ta bayyana.

No comments:

Post a Comment