Tuesday, 12 March 2019

Champions League: Juventus ta lallasa Atletico madrid da ci 3-0: Kuma duk Ronaldo ne ya ci su

Kungiyar Juventus ta lallasa Atletico Madrid da ci 3-0 a wasan da suka buga yau na gasar neman cin kofin zakarun turai kuma tauraron dan wasanta, Cristiano Ronaldo ne yaci duka kwallayen 3.Atletico dai ta ci Juve 2-0 a gidanta kuma waccan rashin nasara tasa ake ganin cewa da wuya Juventus ta tsallake to amma tun kamin wannan wasa na yau, Ronaldo yayi ta baiwa abokanshi na kut da iyalinshi karfin gwiwa zasu ci Atletico, kuma ma wani abin mamaki shine ya rika fadar cewa dama kwallaye 3 zai ci Atleticon kuma sai gashi ta yabbata.

No comments:

Post a Comment