Wednesday, 13 March 2019

Da gaske ne za a dauke CP Wakili daga Kano?

Tun bayan da aka gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 29 a Najeriya, jama'a da dama na ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta a kan cewa rundunar 'yan sandan kasar ta dauke kwamishinan 'yan sandan Kano Mohammed Wakili ta kai shi wata jihar domin ci gaba da aiki.


Mai magana da yawun 'yan sandan reshen jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya shaida wa BBC cewa wannan labarin da ake yada wa ba gaskiya ba ne.

Jama'a da dama a shafukan sada zumunta sun ta mayar da martani kan wannan lamarin tun bayan da aka fara yada wannan jita-jitar.
Wadannan wasu ne daga cikin zantuttukan da ake yi a shafin Twitter kan batun dauke Wakili daga Kano.

Jama'a da dama a Najeriya sun jinjinawa Mohammed Wakili kan irin tsayuwar daka da ya yi a lokacin zaben gwamna da 'yan majalisar jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar.

Shi ma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ll ya jinjinawa kwamaishinan kan irin zage damtsen da ya yi wajen kare dukiyoyi da rayukan jihar Kano.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment