Sunday, 10 March 2019

Dan takarar gwamnan PDP a Kaduna ya fadi zabe a karamar hukumarshi

Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar PDP, Ashiru Kudan yayi rashin nasara a karamar hukumarshi ta Kudan inda gwamna me ci, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya dadashi da kasa.


Me bayyana sakamakon zaben,  Farfesa, Yusuf Dada Amadi ya fadi cewa:

PDP ta samu kuri'u 22,022

APC kuma ta samu kuri'u 28, 624.

A karamar hukumar Makarfi ma El-Rufai ne a kan gaba,

Inda me bayyana sakamakon, Tijjani Abubakar yace:

APC ta samu kuri'u 34, 956

PDP kuma ta samu kuri'u 22, 301

A karamar hukumar Jaba kuwa PDP ce ta lashe zaben.

Me bayyana sakamakon, Ajibike Maruf Ajibola yace.

APC ta samu kuri'u 6, 298

PDP kuma ta samu kuri'u 22, 976.

A karamar hukumar Kaura PDP ce ta yi nasara, me bayyana sakamakon, Dr. Lucas Maude ya bayyana cewa:

APC ta samu kuri'u 8,342

PDP kuma ta samu kuri'u 38, 764.


No comments:

Post a Comment