Friday, 15 March 2019

Dankwambo: Gwamna me Dattako::Gwamnan da ya nuna dattako wurin neman mulki a Arewacin Nigeria kuma bai shirya abunda zai jawo mutuwar talakawan shi ba.

Gwamnan jihar Gombe Dankwambo, yasha kaye a takarar kujerar Sanata a jihar,amma ya hakura kuma bai nemi murde zaben ba, kai yana faduwa ya fito yai ma yan jihar godiya da kuma nuna dangana kan abunda ya faru.


A zaben Gwamna  da yazo,malam Inuwa na APC ya kada Alhaji Nafada wanda gwamnan keso, amma duk da haka  baiyi kokarin murde zaben ba, kai zaben jihar ma yana daga cikin wanda suka bayyana da wuri.

Wannan shine mutunci na siyasa da kuma dan siyasa.

Wannan shine mutumin da ya girmama talakawan shi fiye da neman mulki mai karewa.

Shi dan siyasa a idon talaka kamar rigane in yaga dama ya jefar da ita ko kuma ya wanke yakara sakata ajikin shi,wato in yaga dama yaki zaben ka in kuma yaso yazabe ka ka zarce.

Mulki ba hauka bane,zaka iya faduwa yau goge kai nasara.

Yawancin wanda suka tafka aika aika sune suke kokarin sai sun nada muku wanda zasu mulke ku ko kuma suce dole sai sun zarce.

Abun mamaki kaga Gwamna baitaba damuwa da daruruwan talakawan da ke mutuwa a jihar shi ba, amma kaga ya dage wurin nadama mutane wanda yake so.

Wasu kaga sun fadi zaben amma kaga suna ko amutu ko ai rai wurin tabbatar da sune sukaci.

Duk mai mulkin da yai sanadin mutuwar talakawan shi saboda mulkin shi to wannan baidace yazama jagora ba.

Ana mulkar mutane ne da abunda zukatan su keso bada karfin tuwo ba.

Kowane mutum yakanyi daidai da kuskure, amma abunda wannan Gwamna yayi babban abu ne kuma cigaba ne  a siyasance da Addinance.
Rariya.


No comments:

Post a Comment