Wednesday, 13 March 2019

Duk da bukatar Gwamnan Kano: hukumar 'yansanda ta ce ba zata canja kwamishinan 'yansandan Kano ba

Hukumar 'yansanda ta ce ba zata cire kwamishinan 'yansandan jihar Kano ba duk da bukatar hakan da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar.Daily Nigerian da ta ruwaito cewa gwamnan ya garzaya fadar shugaban kasa inda ya bukaci da a canja kwamishinan 'yansandan, ta ruwaito cewa, wata majiya daga hukumar 'yandandan ta bayyana mata cewa ba za'a canja Muhammad Wakili daga Ka o ba sai lokacin ritayarshi yayi.

Ta kara da cewa, shekarun Wakili 32 yana aiki da hukumar 'yansanda kuma a watan gobe ne zai yi ritaya daga aiki bisa cika shekaru 60 da yayi kamar yanda doka ta tanada, dan haka ba za'a canjashiba sai lokacin ritayarshi yayi.

No comments:

Post a Comment