Sunday, 31 March 2019

Duniyarmu ta haukace: Ana kokarin ceton ranta daga mummunan hadarin da ta yi, ita kuma tana rokon a dauki hotonta a saka a Shafinta na Instagram

A Holan,yayin da suke kokarin ceto ranta,wacce mace da ke cikin mawuyacin hali sakamakon wani kazamin hatsarin da ta yi,ta roki jami'an agaji da su dau hotonta tare yada shi a shafinta na sada zumunta na Instagram,saboda hakan zai matukar birge masoyanta.


Wannan lamarin dai ya afku ne a ranar Alhamis din nan da ta gabata a garin Zaanstreek na yankin Amsterdam,inda babur din da ke dauke da wata mace mai tallar madara ya yi taho mu-gama da wata mota.

A cewar labaran da aka rawaito daga yankin lamarin ya afku,a daidai lokacin da jami'an agaji ke kokarin ceto ranta,macen wacce ke a cikin mayuwacin hali,ta yi ta nanata bukatarta na dau hotonta tare da yada shi a shafinta na sada zumunta na Instragam,saboda hakan zai sa ta samu dubun dubatan "Like".Amma suka ki amince da bukatarta.

An bada cikakken bayani kan wannan lamarin a shafin sada zumunta na Facebook na  'yan sandan a wani labari mai taken "Duniyarmu ta haukace",inda kakakin 'yan sandan yankin Zaanstreek ya ce : "Na daina mamakin irin wadannan ababen.A gaskiya muna rayuwa a wata duniya mai ban ta'ajibi".


No comments:

Post a Comment