Wednesday, 13 March 2019

El-Rufai Bai Je Kano Don Taimakon Ganduje Ba

Wani daga cikin hadiman Gwamnan Jihar Kaduna a cikin masu taimaka masa da abin da ya shafi kafafen yada labarai, Malam Abdallah Yunus Abdallah ya karyata jita jitan da ake yadawa wai Gwamna Malam Nasir El-Rufai yana kano tun Ranar Lahadi domin ya taimaka wa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya lashe zabensa a karo na biyu wanda yake fuskantar barazana daga abokin takararsa Abba. 


Hadimin ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook inda ya nuna cewa zancen ba gaskiya ba ne ta hanyar nuna hotunan da Gwamnan ya karbi takardun sakamakon zabensa da ya lashe daga hannun sakataren gwamnatin Jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Abbas. 

Abdallah Yunus Abdallah ya kara da cewa, Malam Nasir El-Rufai tun ranar  Lahadi yake gida mutane ke cincirondo suna zuwa yi masa murna ganin yadda alkaluma suka bayyana shi zai lashe zaben. 

Sannan ya kara da cewa Gwamna El-Rufai mutum ne da yarda da demokaradiyya, ya yarda da a bar jama’a su zabi shugabanninsu kamar yadda ya nuna a zaben kananan hukumomi ya bar al’umma suka zabi shugabannin da suke so. 

Malam ya kara kafa sheda ta hanyar sanya hotunan da gwamnan ya dauka a cikin daren da abokan arzikinsa da suka zo taya shi murna da da kuma hotunan da ya dauka washegari ranar karban sakamakon zabe.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment