Tuesday, 12 March 2019

Fatalwar Kaddafi ta hana wasu manyan shuwagabannin Duniya sakat

Jiga-jigan siyasa na kasashen yammacin duniya da dama sun tsinci kawunansu a halin kaka-ni-kayi ganin yadda fatalwar tsohon shugaban kasar Libiya,Muhammad Kaddafi ke ci gaba da bibiyar su.


An hambarar da mulkin shugaban kasar Libiya Mu'ammar Kaddafi ta hanyar fakewa da demokradiyya.Abin da ya haifar da tashe-tashen hankula a duk fadin Libiya, durkusar da ma'aikatun gwamnatin kasar daya bayan daya da kuma bai wa kungiyoyin da ke kishin Islama samun gindin zama da cin karansu babu babbaka.

An kashe Mu'ammar Kaddafi a shekarar 2011,amma kawo yanzu fatalwarsa na ci gaba da hana wa shugabanni da dama na kasashen yammacin duniya rumtsawa,inda asirin da yawa daga cikin ke ci gaba da tonuwa.

1-Mutum na farko wanda ya fuskanci gallazawa a washegarin mutuwar Kaddafi shi ne Justin Trudeau wanda al'umar kasarsa ta kira shi da babban  murya da ya gaggauta yin murabus a ranar 27 ga watan Fabrairun da ta gabata,sakamakon samun sa da hannu dumu-dumu wajen gudanar  da wasu haramtattun aiyuka a kasar Libiya.

An fara gudanar da bincike-binciken gano tuggun da shugabannin yammacin duniya suka shirya a kasar Libiya a zamanin da marigayi Mu'ammar Kaddafi ke raye a shekarar 2011.

Kaddamar da wannan binciken ke da wuya,aka gano cewa wani babban kamfanin da shugabanninsa ke da alakar kud-da-kud da tsohuwar gwamnatin kasar Canada ,ya yi kaurin suna wajen bai wa manyan jiga-jigan gwamnatin Kaddafi cin hanci da rashawa don cimma wasu bakaken manufofi nasa.

Kamfanin dai na gaf da samun wasu kungiloli masu tsoka a kasar ta Libiya.Wasu manyan kusoshin gwamnatin Canada sun yi yunkurin tallafa wa dan tsohon shugaban kasar Libiya,Kanar Saadi Kaddafi don ya samu damar ficewa daga kasarsa salim-alim da nufin neman mafaka a Mekziko, a washegarin hambarar da mulkin babansa.

A lokacin da aka fara bincikar wannan kamfanin,Justin Trudeau ba shi ba ne firaministan Canada ,amma kamar yadda Jody Wilson Raybould ta sanar wa duniya,wasu jiga-jigan gwamnatin wancan zamanin sun yi wa Justin Trudeau barazana don ya dakatar da bincike kadaran-kadahan.Haka shi ma Justin Trudeau ya tabbatar da sahihancin wannan batu.

Da yake bayani kan wannan lamarin, Trudeau ya ce : "Ba zan taba yi murabus daga mukamina ba.Ina tabbacin cewar, abokannan aikina sun taka muhimmiyar rawa kana sun nuna kwarewa a wannan binciken.Shi yasa ban taba yarda da matakin da alkali babban kotun Canada ya dauka a baya kan wannan lamarin".

A yau,Justin Trudeau mamban mamba ne a jam'iyyar siyasar da Jody Wilson-Raybould ke wakilta a majalisar dokokin kasar Canada.

Mutum na biyu wanda fatalwar Kaddafi ta hana masa rawar gabar hantsi shi ne,tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy,wanda ake zargi da samun gaggarumin tallafi daga jogaran Libiya a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2007,duk da cewa ya yi watsi da dukannin wadannan tuhume-tuhumen da aka yi masa,inda ya ce maganganu ne marasa tushe da asali.

An fara binciken kan wannan lamarin da hada Nicolas Sarkozy da takwaransa na wancan zamanin, marigayi Mu'ammar Kaddafi na Libiya a shekarar 2013.A watan Nuwamban shekarar 2016,attajirin kasar Faransa kana dan asalin Libiya Ziyada Takiyeddin ya sanar wa shafin watsa na intanet na Mediapart cewa,tsakanin shekarar 2006 da 2007 da karan kansa ya mika wa Nicolas Sarkozy da kuma shugaban tawagarsa,Claude Guéant jakoki uku cike makil da kudaden takarda na yuro 200 da kuma 500.Ziad ya tabbatar da cewa,wannan kudin wanda jimillarsa ya haura yuro milyan 5 ya fito ne daga shugaba Kaddafi.

Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta rawaito cewa,Bashir Salih wanda shi ne shugaban 'yantaccen bankin Libiya ya tabbatar da cewa,Mu'ammar Kaddafi ya tallafa wa Sarkozy da makudan kudade a lokacin yakin neman zaben shugaban kasar Faransa.

Bugu da kari akwai matsalolin da dama da suka kunno kai a kasashen Turai,wadanda dukannin wadannan mishkilolin ke da nasaba da irin muguwar rawar da shugabannin yamma suka taka da kuma wadakar da suka dinka a lokacin mulkin Mu'ammar Kaddafi.

A kasar Beljiyom kuma,Jaridar Le Vif ta kasar ta sanar da cewa, an nemi sama da Yuro biliyan 10 mallakar tsohon shugaban kasar Libiya, Muammar Gaddafi wadanda aka daskare a wasu asusu 4 na bankin Beljiyom, an rasa.

A Shekarar 2011 Majalisar Dinkin Duniya ta bada umarnin a daskare Yura biliyan 15 da a aka wawuro daga Ahli da kuma mukarraban Gaddafi, don daskare su a bankin Euroclear na kasar Beljiyom,har sai abinda hali yayi.

Amma a karshen shekarar da ta gabata, a sa’ailin da wani alkali Brussel mai bincike kan  kungiyoyin  da ke  halatta kudaden haram a Libya, ya waiwayi bankin na Belijiyom sai ya lura da cewa Yuro biliyan 5 kadai suka yi saura, sauran kudaden kuma, babu su babu dalilinsu.

Shin yaya aka yi wadannan makuden kudaden suka fita daga asusun Euroclear ba tare wani ya sani ba?  Shin wa aka bai wa su ? Shin me aka yi da su? Wadannan su ne wasu daga cikin ayoyin tambaya da duniya ta dasa a yanzu haka.

Amma kafin a samu amsoshin wadannan tambayoyin, fatalwarsa Mu'ammar Kaddafi na ci gaba da tsunduma shugabannin kasashen yamma da dama cikin halin ni 'yasu.watakil da nufin daukar fansa kisan wulakancin da suka yi masa.
TRHausa.


No comments:

Post a Comment