Sunday, 10 March 2019

Gwamna Bagudu ya lashe zaben jihar Kebbi

Hukumar zabe me zaman kanta, INEC a takaice ta bayyana gwamna Abubakar Atiku Bagudu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi jiya, Asabar dan haka ya zarce akan kujerarshi.


Farfesa Hamisu Bichi, wanda shine jami'in karbar sakamakon zabe a jihar ya bayyana cewa gwamna Bagudu ya samu kuri'u 673,717 yayinda abokin takararshi, Isah Galaudu na PDP ya samu kuri'u 106,633, kamar yanda NAN ta bayyana.No comments:

Post a Comment