Tuesday, 12 March 2019

Gwamna Ganduje ya nemi a canja kwamishinan 'yansandan Kano

Rahoton Daily Nigerian na cewa gwamnan Kano,Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya garzaya fadar shugaban kasa dan nemam a canja kwamishinan 'yansandan jihar ta Kano.Daily Nigerian ta bayyana cewa ta samu daga majiya me karfi cewa, gwamnan na Kano ya tura wakilai dan suma na kusa da shugaban kasar da suka hada da shugaban jam'iyyar APC,Adams Oshiomhole da Bola Ahmed Tinubu dan samu a canja kwamishinan 'yansandan na Kano, Muhammad Wakili.

'Yansanda dai sun kama magaimakin gwamna  jihar ta Kano tare da kwamishinan kananan hukumomi bisa zargin yunkurin magudin zabe.

Hakanan INEC ta bayyana ranar Asabar, 23 ga watannan a matsayin ranar da zata kammala zaben na Kano wanda jam'iyyar PDP ke kan gaba da sauran jihohin da ba'a kammala zabukan nasu ba.

No comments:

Post a Comment