Saturday, 16 March 2019

Gwamnan Katsina ya baiwa Ummi Duniyarnan Miliyan 6 da dubu dari 5 a matsayin ladar wakar da ta mai

Jarumar fina-finan Hausa, Ummi Abdulwahab wadda aka fi sani da Ummi Duniyarnan ta samu ladar aiki me tsoka daga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari bisa wakar da ta mai.A wani bidiyo da ta wallafa a dandalinta na sada zumunta, anga kudi kimanin miliyan 6 da dubu dari 5 wanda aka saka a asusun ajiyarta na bankin Ja'iz kuma za'a iya jin wata murya na magana a cikin bidiyon inda tace kudin ladar wakar da Ummin ta yiwa gwamnan Katsinane da ya bata, watau Aminu Bello Masari.

A sakon godiya data fitar, Ummi tace ta godewa Allah sannan kuma ta godewa Me gidanta, Nasir Gwangwazo bisa nuna mata hanyar samu da yayiDan kallon bidiyon Dannan nan

No comments:

Post a Comment