Saturday, 16 March 2019

Gwamnatin kano na gina sabon titi a daya daga cikin mazabun da za'a sake zaben gwamna

A yayin da ake fuskantar ranar da hukumar zabe me zaman kanta ta saka na sake zaben wasu runfunan zabe a jihar Kano, gwamna meci dake fuskantar barazanar rasa kujerarshi, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fara aikin zuba kwalta a daya daga cikin mazabun da za'a sake zaben da ta fi yawan jama'a.Kuri'u sama da 141,000 ne ake sa ran za'a kada a zaben da za'a sake kuma mazabar Gama dake karamar hukumar Nasarawa ana kiyasin tana da masu kada kuri'a 40,000, tun da asubahin fari jama'ar mazabar suka ga manyan motocin aikin titi suna zuba kwalta a mazabar, abinda ake ganin kamar yunkurine na jan ra'ayin jama'ar mazabar da gwamnatin jihar ke yi kan su zabe ta a zaben da za'a sake.

Labarin gina titunan mazabar ya dauki hankula sosai harma a shafukan sada zumunta inda ya zama na gaba-gaba da aka fi tattaunawa.
No comments:

Post a Comment