Friday, 29 March 2019

Ina kewar rashin Ronaldo: Juventus ce zata ci Champions League>>Messi

Tauraron dan kwallon kafar kasar Argentina me bugawa kungiyar Barcelona wasa, Lionel Messi ya bayyana cewa tabbas yana kewar Cristiano Ronaldo da ya bar gasar Laliga ya koma Seria A.Messi ya bayyana hakane a hirar da yayi da wani gidan Radio na kasar Argentina inda yace, duk da bana jin dadin yanda nike ga yana lashe kyautuka amma ina jin dadin kalubalantar junan da muke yi.

A wata ruwayar kuma Messin ya kara da cewa yana tunanin Juventus ne zasu dauki kofin Champione league musamman ganin cewa suna da Ronaldo.

No comments:

Post a Comment