Thursday, 7 March 2019

Ina nan da raina ban mutu ba>>Inji matashin da ya sha ruwan kwata saboda murnar cin zaben Buhari

Matashinnan da yayi wanka a cikin kwata ya kuma sha ruwan kwatar dan yin murnar lashe zaben shugaban kasa, muhammadu Buhari ya karyata labarin cewa wai ya mutu, yace yana nan da ranshi karyace kawai aka yada a shafun sada zumuntar yanar gizo ta mutuwar tashi.A hirar da yayi da jaridar Daily Trust, Sani wanda ya fito daga jihar Bauchi ya bayyana cewa, yana nan da ranshi kuma maganar cewa wai an kaishi asibiti karyace, lafiyarshi garas be mutu ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sani yayi alkawarin idan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sake lashe zabe a karo na biyu zai shiga cikin kwata ya kwanta na tsawon wani lokaci sannan ya sha ruwan kwatar. Haka kuwa aka yi, Sani ya cika alkawarin da ya dauka bayan da INEC ta bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya gudana ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata. Hotonshi da ruwan kwatar a jikinshi yayi inkiyar 4+4 ya watsu sosai kamar wutar daji a shafukan sada zumunta.

A ranar Talatane aka ruwaito cewa Sani ya mutu saboda ruwan kwatar da ya sha.

Saidai a hirar da yayi da Daily Trust,  Sani yace yanzu haka yana kan hanyarshi ta komawa Bauchine bayan wani aikin fenti da yaje yi.

Sannan ya bayyana cewa ruwan kwatar da ya sha alkawarine ya cika wanda ya dauka a gaban mutane cewa zai yi idan Buharin ya ci zabe.

No comments:

Post a Comment