Tuesday, 12 March 2019

INEC ta bayyana ranar da zata kammala zabukan jihohin Kano, Sakkawato, Adamawa, Bauchi da sauransu

Hukumar zabe ne zaman kanta, INEC ta bayyana ranar Asabar me zuwa, 23 ga watan Maris a matsayin ranar da zata gudanar da zabuka a jihohin da aka bayyana cewa zaben su be kammalu ba.INEC ta bayyana hakane yau, Talata a babban bornin tarayya ta hannun kwamishinanta, Festus Okoye bayan tarin da ta gudanar akan zabukan.

Jihohin da aka bayyana cewa zabukansu basu kammala ba sune, Benue,Kano, Bauchi, Sakkawato, Filato, da Adamawa.

Festus Okoye ya bayyana cewa, gobe, Laraba INEC din zata bayyana mazabun da za'a sake zabukan a shafinta na sada zumunta, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment