Friday, 15 March 2019

Jadawalin yanda kungiyoyi 8 da suka rage a gasar Champions League zasu kara a Quarter Finals

Man Utd za ta kara da Barcelona a sabon jadawalin da aka fitar na kungiyoyi 8 da za su fafata a Gasar Zakarun Turai a matakin Quarter Finals.


An fitar da jadawalin ne a hedkwatar hukumar UEFA da ke birnin Nyon na kasar Switzerland ranar Juma'a.


Ita kuwa Manchester City zata kara ne da Tottenham sai kuma Juventus da zata hadu da Ajax, sai Liverpool da zata hadu da FC Porto.

Daga nan kuma sai kungiyoyi hudu da suka yi nasara su fafata a wasan kusa da na karshe.

Za a yi wasan karshe ne a ranar Asabar 1 ga watan Yunin 2019, a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid a kasar Spain.

No comments:

Post a Comment