Friday, 22 March 2019

Jama'a ku kawo min dauki sun canja min mijina ba wanda na sani bane>>Matar Gwamna Kaduna

A yayin da ake ta yada labaran karya na cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi hadari kuma rayuwarshi na cikin wani hali na rashin lafiya, gwamnan ya fito ya karyata wancan labari inda ya dangantashi da farfagandar 'yan adawa, sannan kwatsam sai ga hotunan gwamnan sun watsu yayin da yake dawowa daga wata tafiya da yayi.Bayan dawowar gwamnanne sai daya daga cikin matanshi, Hadiza ta bayyana cikin barkwanci a shafinta na dandalin Twitter cewa, jama'ar jihar Kaduna su kawo mata dauki dan kuwa an canja mata mijinta, wanda aka dawo mata dashi kamar sabone kuma yana cikin kwaciyar hankali.


No comments:

Post a Comment