Saturday, 23 March 2019

Jami'an gwamnatin Kano sun hana 'yan Jarida aiki Gama: Sunce su fice ko susa a ji musu: Sun sa 'yan daba kwace kayan aikinsu

Rahotanni dake fitowa daga Zaben raba gardama da ake yi a jihar Kano na cewa a mazabar Gama inda nanne aka fi yawan masu kada kuri'a. Akwai masu zabe dubu 40 na cewa, jami'an gwamnatin jihar da wakilan jam'iyya me mulki a jihar, watau APC ta hana 'yan jarida aikinsu yayin suka sa 'yan daba kwace kayan aikin 'yan jaridar sannan suka bukaci da su fice daga Gamar ko kuma susa a ji musu.Wakilin BBChausa, Nasidi Adamu Yahaya ya bayyana cewa abokin aikinshi dake Gama ya bayyana mai cewa, wakilan gwamnatin jihar Kanon sun gargadi wakilan gidan talabijin din TVC News da su fice daga Gama ko kuma su sa 'yan daba su ji musu rauni.
Haka kuma Nasidi Adamu Yahaya ya kara da cewa, suma wakilinsu na BBChausa wani jami'in gwamnatin jihar, Bappa Babba Dan Agundi, wanda dan majalisar jihane ya sa a ci mutuncin wakilin nasu aka kuma kwace mishi kayan aiki.
Hakanan itama kungiyar Amnesty International ta bayyana cewa wakilan BBC da TVC na fuskantar cin zarafi a hannun jami'an jam'iyya me mulki a jihar Kano wanda hakan be kamata ba dan cin zarafin 'yan jarida ba abune me kyauba.
Hakanan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya bayyana cewa rahotanni na bayyana cewa rikice-rikice sun mamaye zabukan raba gardama dake gudana a sassa daban-daban na kasarnan. Ya kara da cewa sun yi tssammanin cewa tunda inda za'ayi zabukan basu da yawa za'a samu tsari me kyau.
Hakanan shima kakakin PDP ya bayyana cewa, zaben na Kano na cike da rikice-rikice kuma wannan baya kusa da irin zaben da suka gudanar a shekarar 2015 inda ya jawo hankalin jami'an tsaro dasu shawo kan matsalar.

No comments:

Post a Comment