Monday, 11 March 2019

Kaduna ta kafa tarihi a arewa>>El-Rufa'i

Sakamakon zaben gwamnan Kaduna

Gwamnan Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ce Kaduna ta kafa tarihi na zaben mace ta farko a matsayin mataimakiyar gwamna a yankin arewacin Najeriya.


A cikin jawabinsa na amincewa da sake zabensa gwamnan Kaduna a wa'adin shugabanci na biyu, El-Rufai ya gode wa mutanen Kaduna da suka zake ba shi dama sannan kuma yadda suka amince suka zabi mataimakiyarsa mace.

"Kun bijere wa wadanda ba su son ganin an ba mata dama domin nuna basirarsu," in ji shi.

Ya kara da cewa Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe za ta yi aiki tare da kokarin tabbatar da ci gaban jihar Kaduna.

Batun daukar musulma a matsayin mataimakiyar gwamna El-Rufai ya janyo ce-ce-ku-ce tare da kara haifar da zafin siyasar kabilanci a Kaduna.

El-Rufa'i ya doke dan takarar PDP Isa Ashiru wanda ya dauki Kirista a matsayin mataimaki.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment