Monday, 11 March 2019

Kama mataimakin gwamnan Kano: Dama na fada, duk wanda ya taka doka doka zata takashi>>Inji Kwamishinan 'yansandan jihar

Kwamishinan 'yansandan jihar Kano, Muhammad Wakili ya bayyana cewa lamarin kamun da sukawa mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ana kan bincike kuma idan an kammala, doka zata yi aikinta.A hirar da yayi da 'yan jaridu ciki hadda BBC ya bayyana cewa dama fa ya fada cewa duk wanda ya taka doka to doka zata takasho kuma ko wanene, yace ko kun dauka wasa nake?

No comments:

Post a Comment