Saturday, 16 March 2019

Kammala bautar kasar Dan shugaban kasa, Yusuf Buhari ta jawo cece-kuce

Kammala bautar kasar dan shugaban kasa, Yusuf Buhari ta dauki hankulan 'yan Najeriya sosai ta yanda batun ya shiga sahun manyan batutuwan da aka fi tattaunawa akansu a shafin Twitter.Korafe-korafen da ake yi akan kammala bautar kasar dan shugaban kasar suna da yawa:

Wasu na tambayar a wace jiha da wace ma'aikata ya yi bautar kasar tashi, a yayin da wasu ke kare shi da cewa, dan shugaban kasane fa, ta yaya za'ayi tsammanin yayi irin bautar kasar da kowane matashin Najeriya keyi?

Haka wasu sun yi korafi akan cewa an kaiwa Yusuf din takardai shaidar kammala bautar kasarshi har gida wadda suke ganin hakan bai kamata ba.

Wasu kuwa korafin da suke yi shine suna ganin dan shugaban kasa be isa ace ya kammala bautar kasar ba idan aka yi lissafin lokacin da labarin fara bautar kasar nashi ya yadu zuwa yanzu ba.

Gadai abinda wasu ke cewa kamar haka:No comments:

Post a Comment