Wednesday, 27 March 2019

Karanta martanin mahaifiyar Mohamed Salah bayan data ga ya rungumi wata mata

Tauraron dan kwallon kafar kasar Misra/Egypt, Mohamed Salah ya gamu da mahaifiyarshi bayan da ya saka hotonshi yana rungumar wata masoyiyarshi a shafinshi na dandalin sada zumunta.Salah ya saka hoton nashi ne da matar wanda ya dauka lokacin da yake ganawa da masoyanshi, hoton ya dauki hankula sosai lura da cewa ba kasafai aka cika ganin Salah din yana rungumar mata ba.

Daga baya Salah ya ya saka abinda mahaifiyarshi tace mai akan wannan hoton a shafinshi na Instagram, tace mai, da ace na taba ganin babanka yayi irin abinnan da ka yi dana nemi ya sakeni.

Wannan martani na mahaifiyarshi ya dauki hankula sosai.

No comments:

Post a Comment