Thursday, 7 March 2019

Karanta yanda wasu dillalan canjin kudi suka tonawa na hannun damar Atiku asiri kan hadahadar miliyoyin kudaden kasar waje da aka so yin amfani dasu wajan murde zabe

Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta bayyana yanda wasu masu harkar canji a Legas suka tonawa na hannun damar dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar Asiri akan hada-hadar makudan kudin kasashen waje ba bisa ka'ida ba.EFCC dai ta kafe akan cewa kamun da tawa surukin Atiku kuma me kula da hadahadar kudin rukunin kamfanonin Atikun, Babalele Abdullahi ta yi shine bisa hannu da take zarginshi akai na hada-hadar kudin da basa bisa ka'aida, EFCC ta kara da cewa kudin da aka daukesu daga Abuja zuwa Legas dan canjawa an so a yi amfani dasu ne wajan yin magudin zabe.

EFCC ta ce ta kama wasu masu canji guda uku, Abdullahi Shehu, da Abdullahi Munaciki , da Lawal A. Abdullahi wanda suka amshi makudan kudaden na kasar waje dan canjawa yaran Atikun su zuwa Naira dan amfani da su wajan yin magudin zabe amma saboda karancin takardar Nera ba'a samu canja kudin gaba daya ba.

Vanguard ta ruwaito cewa, EFCC ta gano Yuro 41,900,000 daga cikin Yuro 150,000,000 wanda suke da dangantaka da surukin na Atiku, shiyasa ta kamashi, amma tuni ta bayar da belinshi.

Saidai har yanzu lauyan Atiku, Mr. Uyi Giwa-Osagie wanda shi kuma ake tsammanin yayi bayanin zunzurutun kudi har Yuro 26,050,000 da ke da alaka dashi yana hannun EFCC.

Haka kuma EFCC ta ce ta samu cinikayyar miliyoyin daloli tare da wadancan dillan canji wanda suma suka kasa yin bayaninsu,tace dai tana kan bincike dan gano ainihin inda kudin suka fito, sannan idan ta kammala zata gurfanar da wadanda ake zargi a Kotu.

No comments:

Post a Comment