Sunday, 31 March 2019

Ko Manchester City za ta lashe kofuna hudu a bana?

Machseter City na da wasanni 15 da suka rage mata kafin kafa tarihin lashe kofuna hudu a wannan kaka, in da a ranar Asabar za ta fara ke rainin da Fulham a gasar firimiyar Ingila kafin ta hadu da wasu kungiyoyin a wasu gasa daban daban.
Tuni kungiyar ta lashe kofin gasar League Cup, sannan tana da damar sake daga kofin firimiyar Ingila a bana duk da cewa, a yanzu akwai tazarar maki 2 tsakaninta da Liverpool mai jan ragamar teburi.

Kazalika ana ganin Manchester City din ce ke kan gaba wajen samun damar lashe gasar cin kofin zakarun Turai ta bana da kuma gasar cin kofin FA.

Kungiyar za ta fafata da Brighton a matakin wasan dab da na karshe a gasar FA, sannan kuma za ta kai ruwa rana da Tottenham a matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar zakarun Turai.

Manchester City ta samu nasara a wasanni 19 daga cikin 20 da ta buga a baya-bayan nan, abinda yasa ake ganin tana da karsashi na musamman wajen samun nasararori a wasannin da za ta yi a gasa daban daban.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment