Friday, 29 March 2019

Kotu Ta Ba Da Umurnin Kama Shugaban IPOB Nnamdi Kanu

Wata kotun Tarayya karkashin mai shari'a Binta Murtala Nyako a Abujan Najeriya, ta janye belin da ta bai wa shugaban Kungiyar ‘yan aware ta kafa kasar Biafra IPOB, Nnamdi Kanu.


Mai shari’ar har ila yau, ta ba da umurnin a kamo Kanu, hakan kuma na faruwa ne bayan kin bayyana da Kanu ya ki yi a gaban kotu tun bayan da aka bayar da belinsa a watan Afrilun shekara 2017.

Lauyan da ya shigar kara akan tsallaka beli da Kanu ya yi Magaji Labaran shi ne ya nemi haka a lokacin da ya yi wa manema labarai bayani jim kadan bayan da kotu ta yanke hukunci, inda yake cewa, ya nemi haka ne a bisa hurumin kashi 352 karamin kashi na 4 na Kundin manyan laifuka na kasa.

Sanan ya nemi a ci gaba da sauraren kararsa duk da cewa Nnamdi Kanu ba ya nan.

A lokacin da yake bayyana takaicinsa da abin da ya faru a kotun, Ifeanyi Ejiofor, wanda shi ne lauya mai kare Kanu, ya ce kashi 352 na Kundin Manyan laifuka na kasa da kotu ta yi amfani da shi a matsayin hujja na janye belin Kanu, ya ba su hujjar su yi bayanin dalilan da suka hana Kanu zuwa kotu, kuma su na da shi a rubuce.

Ya kara da cewa, amma kotu ba ta ba su daman bayyana haka ba.

Lauyan na Kanu, ya ce shugaban na IPOB yana nan da rai domin suna mu'amala da shi yana mai cewa za su daukaka kara.

To ko me masana shari’a ke cewa dangane da wannan matsaya ta kotu, saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:
VOAhausa.


No comments:

Post a Comment