Thursday, 7 March 2019

Kotu ta ce Abba Kabir zai yi wa PDP takara a Kano

Kotu ta ce Abba Kabir Yusuf ne dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Kano.

Wata Kotun daukaka kara a Kaduna ce ta yi watsi da hukuncin da wata kotun tarayya a Kano ta zartar wacce ta rushe zaben da jam'iyyar PDP ta gudanar a jihar Kano wanda ya bai wa Abba Kabir Yusuf damar zama dan takarar gwamna a jam'iyyar.


Alkalin Kotun daukaka karar a Kaduna Daniel O. Kalio ya jingine hukuncin da kotun Tarayya ta zartar tare da yin umurni ga hukumar zabe INEC kada ta yi aiki da umurnin kotun Kano.

Kotun yanzu ta ba bangarorin biyu kwana biyar su gabatar da bayanai domin yin nazari kafin ta sake yin zama domin sauraren daukaka karar da bangaren Kwankwansiyya ya shigar.


A ranar Litinin ne babbar kotun tarayya a Kano ta rushe zaben na jam'iyyar PDP.

Dan takarar gwamna a jam'iyyar ta PDP, Ali Amin-little, ne ya shigar da karar yana kalubalantar yadda aka yi zaben da har Abba Kabir Yusuf ya zama dan takara.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment