Thursday, 14 March 2019

Kungiya 8 da za su buga quarter final a zakarun Turai

A ranar Juma'a ne za a raba jadawalin wasan daf da na kusa da na karshe wato Quarter Final a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League.


Wannan karon babu batun kungiyar da tafi kokari ko kuma kun fito kasa daya da zarar an zo raba jadawalin, hakan na nufin kowa zai iya haduwa da kowa.

Za a yi bikin raba kungiyoyin ne a birnin Nyon, Switzerland, kuma a nan ne za a yi taron raba jadawalin daf da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai.Ajax
Koci: Erik ten Hag

Fitaccen dan wasanta: Dusan Tadic

Tarihin cin kofin zakarun Turai: Ta dauka sau hudu (1971, 1972, 1973 da kuma1995)

Wannan ne karo na farko da Ajax za ta buga karawar daf da na kusa da na karshe bayan shekara 16, bayan da ta fitar da Real Madrid a wasannin bana.

Barcelona
Koci: Ernesto Valverde

Fitatcen dan wasa: Lionel Messi

Tarihin lashe Champions League: Ta dauka sau biyar (1992, 2006, 2009, 2011 da kuma 2015)

Messi na fatan ya jagoranci Barcelona lashe kofi uku a bana da ya hada da La Liga da Copa del Rey da na kofin zakarun Turai.

Sai dai rabon da Barcelona ta kai wannan matakin tun shekarar 2015 lokacin da ta lashe kofin.

Juventus
Koci: Massimiliano Allegri

Fitatcen dan wasa: Cristiano Ronaldo

Tarihin lashe Champions League: Ta dauka sau biyu (1985 and 1996)

Juventus wadda take ta daya a Serie A na hangen lashe Champions League a baya, inda ta dauko Cristiano Ronaldo wanda ya ci Atletico Madrid kwallo uku ya kai kungiyar wannan matakin.

Liverpool
Koci: Jurgen Klopp

Fitatcen dan wasa: Sadio Mane

Tarihin lashe Champions League: Ta dauka sau biyar (1977, 1978, 1981, 1984 da kuma 2005)

Liverpool wadda take fatan lashe kofin Premier na bana da kofin zakarun Turai ta yi waje da Munich a ranar Laraba, ita ce ta buga wasan karshe a bara.

Manchester City
Koci: Pep Guardiola

Fitaccen dan wasa: Sergio Aguero

Tarihin lashe Champions League: Ta kai wasan daf da karshe (2016)

Daya daga kungiya biyu da ba su dauki kofin zakarun Turai da suka kai wannan matakin. Sai dai kuma Guardiola wanda ya lashe kofin sau biyu a Barcelona na fatan ya yi wannan bajintar a Manchester City.

Manchester United
Koci: Ole Gunnar Solskjaer (rikon kwarya)

Fitatcen dan wasa: Paul Pogba

Tarihin lashe Champions League: Ta dauka sau uku (1968, 1999 da kuma 2008)

Jose Mourinho ya kai United gasar kofin zakarun Turai ta bana daga baya Solskjaer ya karbi aikin, inda ya fitar da Paris St Germain ya kuma kai Quarter Finals.

Porto
Koci: Sergio Conceicao

Fitatcen dan wasa: Eder Militao

Tarihin lashe Champions League: Ta dauka sau biyu (1987 da kuma 2004)

Kungiyar da aka yi mamakin zuwanta wannan matakin na Quarter Final, kuma karon farko ke nan da ta yi wannan bajintar, bayan shekara hudu, inda ta fitar da Roma.

Tottenham
Koci: Mauricio Pochettino

Fitaccen dan wasa: Harry Kane

Tarihin lashe Champions League: Ta kai wasan daf da karshe (1962)

Duk da cewar ba ta dauki sabon dan wasa a bana, sannan ba ta koma filinta da take gyara ba inda take wasa a Wembley, hakan bai hana ta fitar da Borussia Dortmund ba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment