Sunday, 31 March 2019

Kwalba mafi tsada a Duniya

Za a siyar da wata kwalbar Coca-Cola wacce ba a kasafai ake samun ta ba a zunzurutun kudi dalar Amurka dubu 150,wato akalla Naira milyan 54,000,000.


An dai sanar da cewa,a yanzu haka,wannan makekiyar gulbar wacce aka samar da ita a shekarar 1915 ita daya tak a duk fadin duniya.

Cibiyar gwanjon kayayyakin tarihi ta Morphy ta jihar Pensylvanian kasar Amurka ce ta yanke shawarar siyar da wannnan kwalbar ta Coca-Cola a watan Afrilun shekarar bana.
An cewar bayanin da ya fito daga kamfanin Coca-Cola,za a siyar da kwalbar a zunzurutun kudi dalar Amurka dubu 150,000.

An sanar da cewa, wannan kwalbar ta kasance a jerin samfuran farko na kwalaben da Coca-Cola ta samar.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment