Sunday, 31 March 2019

Liverpool ta koma ta daya a Premier

Liverpool ta yi nasarar cin Tottenham 2-1 a wasan mako na 32 a gasar cin kofin Premier karawar hamayya da suka yi ranar Lahadi a Anfield.


Liverpool ce ta fara cin kwallo minti 16 da fara wasa ta hannun Roberto Firmino, yayin da Tottenham ta farke ta hannun Lucas Rodrigues da Silva saura minti 20 a tashi wasan.

Liverpool ta yi nasarar cin kwallo na biyu ta hannun Mohamed Salah daf da za a tashi wasan, kuma hakan ya sa ta samu maki ukun da ya mayar da ita ta daya a kan teburin Premier.


Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta daya kan teburin Premier da maki 79, yayin da Manchester City mai kwantan wasa daya ke mataki na biyu da maki 77.

Ita kuwa Tottenham tana nan a matsayinta na uku da maki 61, daidai da wanda Manchester United take da shi a mataki na hudu.

Idan Arsenal ta ci Newcastle United ranar Litinin, za ta koma ta uku a teburi, inda Tottenham za ta koma ta hudu sai United ta zama ta biyar a teburin gasar bana.

Rabon da Liverpool ta lashe kofin Premier tun 1989/90, bayan da City ita ce mai rike da na bara.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment