Saturday, 30 March 2019

Maiduguri: Rayuwa Cikin Yanayin Zafin Rana

Wasu lokutan hukumar kula da hasashen yanayi ta ‘kasa kan bayyana cewa za a samu budewar rana a jihar Bornon Najeriya, inda wasu lokuta akan kasance a mataki na 42°C ko fiye da haka ma’aunin Celsius .


Duk kuwa da zafin da ake fuskanta mutane suna ci gaba da tafiyar da harkokin rayuwarsu ta yau da kullum a cikin zafin ranar.

Muryar Amurka ta zanta da wasu mutane kan yadda suke kula da lafiyarsu a cikin yanayin zafi. Inda wasu suka bayyana cewa sukan sha ruwa mai yawan gaske da Kankana da kuma Abarba.

Dakta Amina Mohammed Abdullahi, dake zama likita a Asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, ta yi karin haske kan irin cututtukan da mutane zasu iya samu a wannan yanayi na zafi.

A cewar Dakta Amina, lokacin irin wannan zafin babba da yaro kan iya kamura da cutar sankarau, yara kuma kan iya kamuwa da cutar kyanda.

Haka kuma Dakta Amina ta bayar da shawarar shan ruwa mai sanyin gaske kan iya harfarwa da mutane matsala, don haka a samu ruwa madaidaici a rinka sha maimakon mai sanyi.
VOAhausa.


No comments:

Post a Comment