Sunday, 10 March 2019

Maki daya ya rage tsakanin Liverpool da Manchester city: Bayan da Liverpool din suka lallasa Burnley da ci 4-2

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa Burnley da ci 4-2 a wasan Frimiya da suka buga yau,wannan ya baiwa Liverpool damar matsawa kusa da Manchester City dake saman teburi da banbancin maki daya tal tsakaninsu.


Burnley ce ta fara sakawa Liverpool kwallo amma daga baya suka farke suka kuma kara ta hannun Roberto Firmino da Sadio Mane wadanda kowannen su ya ci kwallaye buyi-biyu.


No comments:

Post a Comment