Friday, 15 March 2019

Maryam Yahaya ta yi gagarumar Asara a shafinta na sada zumunta

Jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya ta hadu da masu kutse na shafukan sada zumunta inda suka mata kutse a shafinta na Instagram suka kuma kwaceshi, bayan kwanaki ba'aji duriyarta a shafinta na Instagram ba, Maryam ta bude wani sabon shafin inda ta bayyana cewa an mata kutsene aka kuma kwace tsohon.

Maryam dai ta kere duk wani matashin da matashiya me tasowa a masana'antar fina -finan Hausa wajan yawan mabiya a shafin Instagram, inda ta doshi samun mabiya miliyan daya.

Sannan kuma itace jarumar da ta fi samun mabiya da sauri fiye da kowane jarumi da jaruma a shafin nata na Instagram da aka mata kutse.

Da ta kai mabiya miliyan 1 da ta kafa tarihin kasancewa matashiyar jarumar da ta shiga sahun manyan jarumai masu mabiya miliyan daya, sannan kuma matashiyar jarumar da ta samu mabiya miliyan daya da sauri fiye da kowane jarumi a masana'antar.

Maryam Yahaya dai ta fito an santane sosai a fim din Mansur, daganan ta fito a fina-finai irinsu, mijin yarinya, Sabon Mujadala, Mariya, dadai sauransu.

Abin jira a gani shine ko maryam zata sake samun mabiya da sauri a sabon shafin nata na Instagram kamar yanda ta samu a tsohon da aka mata kutse? Lokaci ne kadai zai bayyana haka ga me rai.

Muna tayata jaje da fatan Allah ya kiyaye na gaba.

No comments:

Post a Comment