Saturday, 16 March 2019

Matan da ke dauke da cutar HIV AIDS sun yi barazanar yada ta a Najeriya

Yayinda mahukunta a Najeriya su ka ce kasar ta koma matsayi ta hudu a tsakanin kasashen duniya da su ka fi yawan masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDs wasu mata da ke dauke da cutar a Maiduguri sun yi barazanar ci gaba da yada ta saboda yadda su ke zargin an yi watsi da su ba a taimaka musu. A cikin rahoton da wakilin RFIhausa, Bilyaminu Yusuf ya hada matan dake dauke da cutar a Borno sun bayyana cewa sun samu wannan cutane dalilin rikicin Boko Haram kodai an musu fyade kokuma sun bayar da kansu dan samun kudi da zasu biya bukatunsu na yau da kullun.

Wata mata da RFI ta yi hira da ita ta bayyana cewa suna da yara dake zuwa makaranta suna kuma zaune a gidan haya sannan basu da tallafin da suke samu daga gwamnati, an yi watsi dasu dan haka a cikin irin wannan hali duk namijin da yazo da bukatarshi ya bata kudi to zata bada kanta gareshi.

Mahukuntan jihar akan kula da cutar ta HIV sun bayyana cewa, za'a shawo kan matsalar nan bada jimawaba.

No comments:

Post a Comment