Sunday, 10 March 2019

Mutum mafi tsufa a Duniya na a Japan

Wata tsohuwar Japan mai shekaru 116 da haihuwa, ta kafa tarihin a littafin Guinness World Records wanda ke adana bayanan abubuwa masu ban ta'ajabi, a matsayin mutum mafi tsufa a duniya.


Guinness World Records ta ayyana dattijiyar mai suna Kane Tanaka wanda a yanzu haka yake ci gaba da rayuwa a gidan gajiyayyu na Fukuokada da ke kudumaso yammacin Japan,a matsayin mutum mafi tsufa a duniya karkashin sa-idon shugaban ma'aikatar magajin gari na yankin.

Tsohuwar mai shekaru 116 da haihuwa wacce ke sha'awar wasannin kwallon tebur da darar Othello na farkawa daga barci a kowace safiya a daidai karfe 06:00.

An haifi Tanaka wacce  'yar auta ce a muhalli da ke kunshe da 'ya 'ya 8, a ranar 2 ga watan Janairun shekarar 1903.A shekarar 1922 dattijiya Kane Tanaka da mijinta Hideo Tanaka sun haifi 'ya 'ya 4,inda suka reni wasu karin 'ya 'yan biyu wadanda suka karbo daga gidan marayu.

Kafin Tanaka ta cimma wa wannan matsayin, tsohuwar kasar Japan Chiyo Miyako mai shekaru 117 da haihuwa  wacce ta kwanta dama a watan Yulin bara ce ta kasance mutum mafi tsufa a duniya.

A cewar littafin Guinness World Records,mutumin da ya fi tsawon rai a duniya shi ne Jeanne Louise Calment ta kasar Faransa wacce ta share shekaru 122 a doron kasa.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment