Wednesday, 13 March 2019

Na taba aske gashi na saboda 2Pac, yanzu kuma zan sake askewa saboda Buhari>>General BMB

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, wanda ake kira da General BMB ya bayyana cewa zai cika Alkawarin da ya dauka na aske sumarshi da ya dade yana gayu da ita saboda cin zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari.BMB ya bayyana cewa a baya ya aske sumar tashi saboda tsohon mawakin kasar Amurka, Marigayi, 2Pac sannan yanzu zai sake aske sumar tashi saboda Buhari. 


Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba zai cika wannan alkawari da ya dauka.

BMB na daya daga cikin masoyan shugaba Buhari a masana'antar Kannywood inda har ya fitar da wata kungiya ta masoya Buharin da ya sakawa suna VOBA.

No comments:

Post a Comment