Saturday, 16 March 2019

Nan gaba kadan mazan Duniya zasu kare


"Saura kiris a nemi maza a rasa"
Jami'ar Kent ta kasar Ingila ta gano cewa, nan da wasu shekaru masu zuwa,maza zasu gushe kwata-kwata daga doron duniya,kamar ba a taba halittar su ba.


Kwayar halittar Y wacce ita ce ke silar samar da jinsin maza,zai iya gushewa daga doron duniya nan da wasu shekaru masu gabatowa,wanda hakan na nufin gushewar maza kwata-kwata daga duniyarmu,inji wani kwararren masanin ilimin kwayoyin halittu,Darren Griffin na jami'ar birnin Kent da ke kasar Burtaniya.
Makomar kwayar halittar Y na ci gaba da tayar da hankalin masanan duniya.Abinda yasa a rubutun da ya wallafa a wata makala mai taken "Science Alert",kwararren ya bayyana cewa,matsalar Y na da nasaba ne da yadda kwayar halittar ta kasance ita daya tak a gangar jikin dan adam.Ba ta da mai kama ko kuma wacce ke da fasaloli irin nata
Haka zalika, masanan sun bayyana tasirin barasa kan lalacewar fasalolin kwayar halittar Y,wacce ke dakatar da ninkuwar ta a tsawon shekaru, akasin yadda sauran kwayoyin halittu ke hayayyafa da kuma sabuntuwa.
Abinda yasa M.Griffin ya ce,akwai yiwuwar kwayoyin halittun da ke nasaba da samar da jinsin maza su lalace da kuma bacewa ga baki daya daga doron duniya.
Abinda yasa tuni masana suka dasa ayar tambaya kamar haka: Shin ko yaya rayuwa za ta kasance,idan har ba namiji ko daya a duk fadin duniya?
TRThausa.

No comments:

Post a Comment