Tuesday, 12 March 2019

RA'AYI: Yanzu Dai Kam Babu Wata Dimokuradiyya A Nijeriya


Me ya sa Duk Inda Jam'iyar APC Ta ci Zaben Suka Sanar Da Cinye Zaben Amma Kuma Duk Inda PDP Ke Kan Gaba Sun ce Wai Ba'a Karasa ba?
Ga Misali.

*Jihar Kano an dakatar yayin da PDP take kan nasara.

*Jihar Sokoto an dakatar yayin da PDP take kan nasara.

*Jihar Filato ma an dakatar yayin da PDP take kan nasara.

Jihar Taraba an dakatar yayin da PDP take kan nasara.

Jihar Adamawa an dakatar yayin da PDP take kan nasara. 

Jihar Bauchi an dakatar yayin da PDP take kan nasara.

Jihar Rivers an dakatar yayin da PDP take kan nasara.

Jihar Imo an dakatar yayim da PDP take kan gaba.

Kai tsaye an fadi wanda yayi nasara a Jihar Kaduna saboda APC ce ta ci. Haka ma Jihohin Niger, Kebbi, Katsina, Gombe, Jigawa, Kwara, Yobe, Borno da Zamfara.

Maganar Gaskiya Wannan Sharrin Gwamantin Tarayya ne Da Ba ta Son Zaman Lafiya Al'ummar ta.

Me ya sa Duk Inda Jam'iyar APC Ta ci Zaben Suka Sanar Da Cinye Zaben Amma Kuma Duk Inda PDP Ke Kan Gaba Sun ce Wai Ba'a Karasa ba

Kuma Wai A Haka Dimokuradiyya Ake yi. Bai Kamata Ku Rinka Wahalar Da Jama'a ba Matukar Kuka san Kama Karya Za ku yi.

Maganar Gaskiya fa Yanzu Ko Akan Waye Za mu Fade ta Komai Dacinta.

Muna Addu'a Allah Ka Ceto Dimokuradiyya A Nageriya...

Wallahi Ku Tsaya Ku Gani Ta Karfi Sai Sun Kwace Wannan Zaben. Kai Jama'a Lamarin Buhari Yana Bani Tsoro Wai Kuma Mai Gaskiya Amma Yana Kallo Ko nace Ya Saka Sai Kama Karya Ake Da Rayuwar Al'ummar Nijeriya.

Kuda Allah M Inuwa MH ISMOG

No comments:

Post a Comment