Sunday, 31 March 2019

Ronaldo ya karfafa giwar masoyanshi kan warkewa daga ciwon da ya ji


cristiano ronaldo, juve, esulta, pugno, spalle, 2018/19
A yayin da aka saka idanu dan ganin ko tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo zai samu warkewa daga ciwon da ya samu kamin babban wasan kungiyar da Ajax na cin gasar Champions League dake tafe, Ronaldon ya baiwa masoyanshi karfin gwiwa akan dawowar tashi.

A wani sako daya wallafa a shafinshi na Instagram Ronaldo ya bayyana cewa yana aiki tukuru dan ganin ya warke daga ciwon da ya ji.

A ranar 10 ga watan Aprilu ne Juventus zata hadu da Ajax.

No comments:

Post a Comment