Sunday, 10 March 2019

Sakamakon zaben Gwamnan jihar Sakkwato: Gwamna Tambuwal na kan gaba da kananan hukumomi 5 cikin 6 da aka sanar da sakamakonsu

A sakamakon zaben gwamna na jihar Sakkawato dake ci gaba da bayyana, gwamnan jihar me ci,Aminu Waziri Tambuwal na kan gaba inda ya lashe zaben kananan hukumomi 5 a cikin 6 da aka bayyana.


Kananan hukumomin da Gwamna Tambuwal ya lashe sune: Bodinga, Binji, Silame, Kware, Tureta, yayinda abokin karawarshi na jam'iyyar APC, Ahmed Aliyu ya lashe zaben karamar hukumar Rabah.Ahmed Aliyu ya samu kuri'u 16,535 a karamar hukumar Rabah, yayinda gwamna Tambuwal ya samu kuri'u 13,232.

A Tureta kuwa, PDP ta samu kuri'u 13,017, yayinda APC ta samu 11,454.

A Bodinga kuwa PDP ta samu kuri'u 21,416 yayinda APC ta samu 20,779.

A Binji PDP ta samu kuriu, 12, 367 yayinda APC ta samu 10, 699.

A karamar hukumar kware, PDP ta samu, 20, 111 yayinda APC ta samu 19,001.
Premiumtimes.

No comments:

Post a Comment