Tuesday, 12 March 2019

Sakamakon zaben Gwamnoni a jihohin Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, a matakin jihohi ta fara sanar da gwamnonin da suka yi nasara a zaben ranar Asabar 9 ga watan Maris.


media
Cikin sanarwar sakamakon da INEC ta fitar a jihar Lagos ya nuna cewa dan takarar Jam’iyyar APC mai mulki Babajide Sanwo-Olu ya yi nasara kan abokin takararsa na Jam’iyyar PDP Jimi Agbaje da kuri’a dubu 739 da 445 yayinda shi kuma Mr Agbaje ya samu kuri’u dubu 206 da 141.
A bangare guda shi ma dan takarar gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar da ke neman zagaye na biyu karkashin Jam’iyyar ta APC ya yi nasara da kuri’u dubu 810 da 933 yayinda abokin takararsa na Jan’iyyar PDP Aminu Ibrahim Ringim ya samu kuri’u dubu 288 da 356.
A jihar Kwara ma dan takarar Jam’iyyar APC Abdurrahman Abdulrazaq ne ya yi nasara da kuri’u dubu 331 da 546 yayinda abokin takararsa na Jam’iyyar PDP Abdulrazaq Atunwa ya samu kuri’u dubu 114 da 754.
A jihar Gombe dan takarar Jam’iyyar APC Inuwa Yahaya ne ya yi nasara a zaben Gwamnan da kuri’u dubu 364 da 179, yayinda abokin takararsa na Jam’iyyar PDP Sanata Usman Nafada ya samu kuri’u dubu 222 da 868.
A jihar Abia kuwa dan takarar Jam’iyyar PDP Okezie Ikpeazu ne ya sake yin nasara a zaben Gwamnan da kuri’u dubu 261 da 127 yayinda dan datakarar Jam’iyyar APC Uchechukwu Ogah ya sha kaye da kuri’u dubu 99 da 574.
Ga dai yadda sakamakon zaben ya kaya a jihohin Najeriyar tsakanin manyan jam'iyyun da ke hamayya da juna na APC da PDP.
JIHOHIAPCPDP
ABIA99,574261,127
JIGAWA810,933288,356
GOMBE364,179222,868
KWARA331,546114,754
LAGOS739,445206,141
AKWA IBOM171,978519,712
CROSS RIVER131,161381,484
EBONYI81,703393,043
ENUGU99,574449,935
KATSINA1,178,864488,621
KEBBI673,717106,633
NIGER526,412298,065
OYO357, 982515, 621
YOBE444,01395,703
KADUNA1,045,427814,168
ZAMFARA534,541189,452
DELTA215,938925,274
OGUN241,67070,290
   

RFIhausa.

No comments:

Post a Comment