Friday, 15 March 2019

Sakon Adam A. Zango ga abokan sana'arshi

Tauraron fina-finan Hausa Kuma mawaki, Adam A. Zango ya yi wani rubutu inda ya aika sako ga abokan sana'arshi na masana'antar Kannywood, musamman akan irin dambarwar siyasar da ake damawa, ya bayyana cewa idan Ganduje ya fadi zabe ko kuma Abba be ci ba to akwai wanda Kano zata gagaresu zama ko kuma su zauna cikin kunci.Ga abinda ya rubuta kamar haka:

KANNYWOOD DIN YANZU BA KAMAR TA BAYA BACE, TA YANZU SUNANTA KASUWAR BUKATA. 
MAI KUDI KO DAUKAKA KO BUDEWA MUTANE HANYAR DA ZASU SAMI KUDI SHINE MAI FADA AJI. IDAN KA RASA DAYA DAGA CIKI TOH TAKA TA KARE. DON HAKAN YA FARU A DA MUTANE DA DAMA A CIKIN MASANA'ANTAR
.
SANNAN KUMA TARIHI YA BAR MUKU LITTAFIN DA ZAKU KARANTA LABARIN KANNYWOOD.
_MISALI;
YAU INA IBRO
YAU INA AHMAD S. NUHU 
YAU INA ASHIRU NAGOMA
YAU INA AL'RAHUS 
YAU INA H.R.B
YAU INA ABDULAZIZ DAN SMALL
YAU INA AHLAN
YAU INA CIROKI
YAU INA USMAN MU'AZU
YAU INA ABUBAKAR SANI 
YAU INA ADAMU NAGUDU 
YAU INA SADI SIDI
YAU INA ALI BABA YAKASAI 
YAU INA IBRAHIM DANKO
YAU INA ZAINAB INDOMI .
DUK WADAN NAN MUTANE NE DA AKACI MORIYAR SU KUMA AKA JUYA MUSU BAYA WASU KUMA SUN MUTU, WASU KUMA BASU DA LAFIYA, DON HAKA AMFANINSU YA KARE.
.
WASU A DALILIN WADAN NAN SUKAYI AURE, SUKAYI MOTA, SUKA GINA GIDA, SANNAN SUKE CIYAR DA IYAYENSU.
.
INA TUNATAR DAKU NE SABODA NI INA DA MAFITA KO AN DAINA FILM.
.
BABBAR MATSALAR KUMA SHINE MATUKAR GADUJE YA SAKE HAWA GWAMNAN KANO TOH WASU FA ZAMAN KANO YA KARE IDAN KUMA SUKA ZAUNA TOH ZASUYI RAYUWA CIKIN TAKURA DA TSORO. HAKA ZALIKA IDAN ABBA YACI HAKAN NE ZAI KASANCE SABODA SIYASAR WANNAN SHEKARAN TA BANBANTA DA DUK WADANDA AKAYI A BAYA.
TOH DUK MAI YA JANYO MANA HAKA? KWADAYI DA SON ZUCIYA.
.
YAN UWANA 
INA MU ZAMU RINKA SON JUNANMU KAMAR YADDA MUKE SON YAN SIYASA.
.
INA MA ZAMU RINKA YIWA MASANA'ANTARMU ADDU'A KAMAR YADDA MUKE YIWA YAN SIYASA.
.
INA MA ZAMU RINKA KARE MUTUNCIN JUNAN MU KAMAR YADDA MUKE KARE NA YAN SIYASA
.
INA MA ZAMU RINKA TAYAR DA JIJIYAR WUYANMU IDAN AKA TABA IYAYEN GIDAMMU KAMAR YADDA MUKE YIWA YAN SIYASA. .
INA MA ZAMU RINKA KUKAN BAKIN CIKI IDAN ABOKIN SANA'ARMU YA SHIGA MUGUN HALI KAMAR YADDA MUKE YIWA YAN SIYASA. .
INA MA ZAMU RINKA FADIN ALKHAIRAN JUNAMMU KAMAR YADDA MUKE FADIN NA YAN SIYASA.
.
INA MA ZAMU RINKA TALLATAWA JUNAMMU HAJAR SU KAMAR YADDA MUKE TALLATA JAM'IYYAR YAN SIYASA. .
INA MA ZAMU RINKA HADA KAWU NANMU KAMAR YADDA MUKE HADAWA IDAN AKA KIRAMU VILLA. 
RUWA CIKIN LUDAYI YA ISHE MAI
.
INA MA ZAMU RINKA TURURUWAR ZUWA BIKI, JANA'IZA, DAURIN AUREN JUNANMU KAMAR YADDA MUKE TURURUWA ZUWA WAJEN CAMPAIGN DIN YAN SIYASA.
(RAWAHUL ZANGO)

No comments:

Post a Comment