Saturday, 2 March 2019

Sakon Alan Waka ga Adam A. Zango bayan kammala zaben shugaban kasa

Tauraron mawakin Hausa, Aminu Alan Waka ya aikewa da abokin aikinshi, Adam A. Zango da sako na musamman bayan kammala zaben shugaban kasa da aka yi a makon jiya, ga sakon kamar haka:
Ina tuna Abubuwa da yawa da suka hadamu da kai Adamu kama daga kalmar shahada da yaren Hausa da zama a yanki daya ga Uwa Uba Sana'a Iri daya. Ina tuna haduwarmu a tarukan zumunci na waka ko Dandalin karbar kambum karramawa da makamantansu, ina tuna yarda mutane ke harsashenmu tamkar uwa daya uba daya dun abinda ya Sameka ai ta bugo waya ana so a ji dahir daga gareni don zaton ni da kai abu daya ne, Saboda Sana'ar Waka. Me zai sa muga baiken juna a yayin da ra'ayinmu ya banbanta a kasuwar Bukata?

Ina taya ka jaje na tallar abinda ka dauko baka kai ga nasara ba, Kuma ina yi maka bushara da hakuri da wautar masu wauta, Ina karfafa tunaninka da yabawa musamman yarda ka bayyana fatan Alkhairi ga wanda Allah ya baiwa Nasara. Akarshe Ina fatan zamu hadu karkashin kishin kasarmu Nigeri kasa Daya Al'umma Daya. Mu kuma dawo fagen Fama na Sana'armu don gani wanne tudu wanne gangare zamu kai ga ci, Don cigaba da Samarwa kanmu Mafita a harkar taro sisi. Allah ya baiwa kasarmu zaman lafiya da bunkasar arziki, ya baiwa shugabanmu jagoranmu lafiya da nisan kwanan da zai waiwayemu da ayyukan cigaba a arewa.
No comments:

Post a Comment