Friday, 15 March 2019

Sanata Shehu Sani ya bayyana abin da Gwamnatin Buhari da sauran gwamnatocin da suka gabata suka kasa yi wanda Jonathanne kawai yayi

Sanatan Kaduna ta tsakiya me barin gado, Sanata Shehu Sani ya bayyana abinda gwamnatocin baya dama me ci suka kasa yi in banda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.Shehu Sani yace gwamnatocin baya dama me ci basu son gyara dokokin zabe saboda suna amfana da rashin kyawun dokokin. Ya kara da cewa, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ne kawai shugaban da ya taba nada shugaban Hukumar zabe, INEC da be sani ba kuma be taba haduwa dashi ba sannan ya amince a yi amfani da fasahar da ta kawo karshen mulkinshi.

No comments:

Post a Comment