Sunday, 10 March 2019

Sanwo Olu na APC ya lashe zaben Legas

Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta bayyana dan takarar jam'iyyar APC na jihar Legas, Babajide Sanwo Olu a matsayin wanda ya lashe zaben jihar inda ya kayar da Jimi Agbaje na PDP.
Bayan bayyana Sanwo Olu a matsayin wanda yayi nasara, gwamna me barin gado, Akinwunmi Ambode ya tayashi murna.

Haka shima dan takarar jam'iyyar PDP,Jimi Agbaje ya kira Sanwo Olun ya tayashi murna, kamar yanda ya bayyana da kanshi inda yaje Jimi ya kirashi ta waya ya tayashi murna.

No comments:

Post a Comment