Sunday, 31 March 2019

Sarkin Kano ya bayyana matsayinshi akan nasarar Gwamnan Ganduje akan Abba

A jiya, Asabarne me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ya jagoranci addu'a a babban masallacin jihar Kano akan Allah ya taimaki gwamnan Kanon, Dr. Abdullahi Umar Ganduje wajan gudanar da mulkinshi a karo na biyu.Vanguard ta ruwaito cewa, Sarki Sanusi ya jawo hankalin gwamnan akan yin yafiya ga wanda suka saba masa domin harkar mulki saida kauda kai da yafiya.

Ya kara da cewa an gudanar da addu'arne akan Allah ya taimaki gwamna Ganduje a mulkinshi karo na biyu, yace, gwamnan ya rika bincikar labaran da suke zo masa, dan wasu na kusa da shi sukan zo su fadi wani abu ko yi wani abu da bashine yace ayi ba sai hakan yasa aita watsa jita-jitar cewa shine yayi.

Yace zasu ci gaba da addu'ar Allah ya zaunar da Kano lafiya ya kuma baiwa Gwamnan Nasara a mulkinshi ya kuma bashi ikon rungumar kowa dan a tafi tare.

No comments:

Post a Comment