Saturday, 30 March 2019

Shari'ar Musulunci ta fusata 'yan fim

Dan fim din Amurkan nan George Clooney na kira da a kaurace wa wasu otal-otal na alfarma guda tara da ke da alaka da Brunei, bayan da kasar ta ce za ta rika yanke hukuncin kisa ga masu luwadi da zina.


Mista Clooney ya ce sabbin dokokin sun keta haddin 'yancin dan adam.

Ya ce: ''Brunei tana bin tsarin mulkin Mulukiya ne wanda kaurace wa otal-otal din ba zai yi wani babban tasiri ba wajen ganin an sauya dokokin, to amma za mu taimaka ne wajen wannan keta 'yancin dan adam?''


Daga ranar uku ga watan Afrilu, 'yar karamar kasar ta Kudu maso Gabashin Asiya za ta rika aiwatar da hukuncin bulala ko jefewa ga wadanda aka samu da laifin luwadi ko zina.

A shekara ta 2014 Brunei ta kasance kasa ta farko a yankin Kudu maso Gabashin Asiya da ta ayyana amfani da tsarin Shari'ar Musulunci, duk da yadda aka yi ca a kanta da suka.

Dan fim din na Hollywood ya ce, kamata ya yi masu hamayya da dokar su kaurace wa rukunin otal-otal din Dorchester da ke Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma Italiya, wadanda mallakar Hukumar Zuba Jari ce ta Brunei.

Kasar Brunei wadda ke tsibirin Borneo tana karkashin mulkin Sarki Sultan Hassanal Bolkiah ne kuma ta samu arzikinta ne ta hanyar sayar wa kasashe mai da iskar gas.

Sarkin shi ne ya mallaki Hukumar Zuba Jari ta Brunei, wadda ta mallaki wasu daga cikin manyan otal-otal na kasaita na duniya.

Daga cikinsu akwai Dorchester a birnin landan da kuma Otal din Beverly Hills a birnin Los Angeles.

Mista Clooney ya ce ya sauka a wasu da dama daga cikin otal-otal din a bisa rashin gudanar da binciken wanda ya mallake su.

Ya kara da cewa: '' A duk lokacin da muka sauka ko muka yi taro ko kuma muka yi liyafa a daya daga cikin wadannan otal-otal guda tara, to muna sa kudi ne kai tsaye a aljihun mutanen da suka zabi aiwatar da hukuncin jefewa ko bulala ga 'yan kasarsu.''

Wasu fitattun mutanen su ma sun ce za su kaurace wa rukunin otal-otal din na Dorchester, domin nuna goyon bayansu ga matakin hamayya da hukuncin Shari'ar Musuluncin a kan 'yan luwadi da masu zina.

Mai shirya fina-finai Dustin Lance Black ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: ''Idan ka ci gaba da zama ko zuwa Otal din Beverly Hills, to kana da laifin taimaka wa wadannan masu kisan kai.''

Shi ma editan harkokin duniya na BBC John Simpson ya tabbatar da cewa ba zai rika zuwa otal-otal din na Brunei din ba.

A shekara ta 2014 Ellen DeGeneres da Stephen Fry sun lashi takobin kauracewa daga hadakar da ta mallaki otal-otal din saboda dokokin hukunta 'yan luwadin na Brunei.

'Yan gidan Sarautar Brunei din suna da dimbin arziki, kuma al'ummar tsibirin wadanda yawancinsu 'yan kabilar Malaysia da Indonesia ne suna samun kyautar kudi daga gwamnati kuma ba sa biyan haraji.

Kusan shekara biyar da ta wuce ne Sarkin ya bullo da tsarin amfani da Shari'ar Musulunci, wadda za a rika aiki da ita a hankali a hankali cikin shekaru, har ta zama jiki.

A karkashin sabuwar dokar za a rika yanke wa barayi hannu, idan kuma aka kara samun mutum da laifin satar za a yanke masa kafa.

Lokacin da Sarkin mai shekara 72, daya daga cikin manyan attajiran duniya, ya sanar da bullo da dokar Shari'ar ya kira ta da wani bangare na tarihin kasarsu mai girma.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment