Thursday, 7 March 2019

Shewar sunana da 'yan madrid suka rika yi abin Alfaharine>>Mourinho

Tsohon me horas da kungiyar Real Madrid, Jose Mourinhi ya bayyana cewa abin alfaharine a gareshi irin yanda masoyan kungiyar Madrid din ke ta shewar sunanshi bayan fitar dasu da Ajax ta yi daga gasar cin kofin turai.A ranar talatar data gabatane, Ajax ta bi Madrid har gida ta zazzaga mata ci 4-1, bayan kammala wasanne magoya bayan kungiyar ta Madrid suka hau kan tituna suna ta shewar sunan Mourinhon a wani yanayi da ke nuna alamar kewar kocin.

Tsohon shugaban kungiyar, Ramon Calderon ya bayyanawa Sky Sport cewa, Mourinhone koci na daya da Madrid din take nema dan ya sake dawowa horar da 'yan wasanta kuma tuni har kungiyar ta fara tuntubarshi.

Saidai a hirar da yayi da wani gidan talabijin na sifaniya, El Chiringuito, Mourinho yace ihun da masoyan Madrid din suka rika yi na sunanshi abin alfaharine kuma kada a manta cewa Madrid na da me horas wa wanda kuma hakan shima ya isa abin alfahari.

Dangane da maganar tuntubarshi da akace kungiyar ta yi, Mourinho yace ko kadan bai fara magana da Madrid din ba akan komawa horas da 'yan wasanta ba, jita-jitace kawai wanda kuma hakan bashi da kyau a harkar kwallon kafa.

No comments:

Post a Comment