Friday, 8 March 2019

Shugaba Buhari ya bayyana abinda zai yi kamin ya kammala wa'adin mulkinshi na biyu

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana abinda zai yi kamin kammala wa'adin mulkinshi na biyu, da farko dai yace idan ya kammala mulkin zai koma mahaifarshi, Daura Jihar katsinane.Saidai kaminnan ya bayyana cewa, zai yi aiki tukuru wajan ganin ya samarwa da 'yan Najeriya tsaro, ayyukan yi, yaki da cin hanci, da kuma samar da ababen more rayuwa, shugaban yace, zai jajirce fiye da yanda yayi a wa'adin mulkinshi na farko, kuma ba zai baiwa 'yan Najeriya kunya ba.

No comments:

Post a Comment