Thursday, 7 March 2019

Shugaba Buhari ya kai ziyarar farko jihar Kaduna tun bayan lashe zabe da yayi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Kaduna inda ya kaddamar da wata cibiyar saka ido ta jirgin sama a jihar, gwamnan jihar,Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne ya tarbi shugaban ta hanyar durkusa har kasa kamar yanda ya saba.Saidai tun kamin zuwan shugaban shugaban jihar, labari ya watsu cewa zai zo jihar ne dan rokawa gwamnan El-Rufai goyon bayan jama'ar jihar a zaben gwamna da za'ayi ranar Asabar.

Shugaban ya samu kyakkyawar tarba daga mutane.
No comments:

Post a Comment